29 Satumba 2025 - 20:28
Source: ABNA24
Sojojin Isra’ila 2 Ne Suka Sheka Lahira 9 Sun Jikkata A Harin Gaza Na Yau + Bidiyo

A cewar wadannan kafafen yada labarai, wani makamin roka da aka harba ya afkawa gungun sojojin Isra’ila, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da jikkata. Majiyar Ibraniyawa ta kuma ruwaito cewa, an dauke wadanda suka jikkata a lamarin da jirgin helikwafta zuwa asibitin Soroka.

Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun nakalto dakarun gwagwarmaya a  Gaza sun 2 daga cikin sojojin mamaya ya zuwa yanzu tare da jikkatar wasu da dama. Majiyoyin Ibraniyawa sun yi ikirarin cewa akwai yiwuwar batar wasu daga wadanda suka jikkata a harin daya gabata a Gaza

Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayyana cewa an kashe sojojin gwamnatin kasar 2 tare da jikkata wasu mutane 9 a wani harin roka da aka kai a arewacin zirin Gaza.

Wannan harin ya faru a sa’I daya da lokacin ganawar Netanyahu da Trump

Kafofin yada labarai na yaren yahudanci sun rawaito cewa ana ci gaba da kai harin kan titin Al-Jala da ke birnin Gaza. Kafofin yada labaran sun kuma bayar da rahoton cewa, jiragen sama masu saukar ungulu na soji sun sauka a asibitin Yakhlov kuma suna jigilar sojojin da suka jikkata daga zirin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha